ABNA24 : A ranar Assabar data gabata ne yarjejeniyar fahimtar junar watanni uku dake tsakanin hukumar ta IAEA da kuma Iran, ta kawo karshe.
Amma daga bisani bangarorin biyu sun amince da tsawaita yarjejeniyar da wata guda, domin bada dama samun nasara ga tattaunawar da ake ta farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran dake gudana a Vienna.
Hakan, na nufin hukumar ta (IAEA) za ta ci gaba da samun hotunan bidiyon da kyamarori ke dauka a cibiyoyin nukiliyar Iran.
342/